Labarai

Covid – 19 : Makarantun Kudi A Najeriya Sun Bukaci Gwamnatin Tarayya Da Ta Basu Rancen Kudade.

Spread the love

Daga Miftahu Ahmad Panda

Gamayyar Mamallakan Makarantu Masu Zaman Kansu a Kasarnan sun Bukaci Gwamnatin Tarayya data Basu Rancen Kudade ba tare Da Saka musu Kudin Ruwa Mai yawa ba Domin Dai Suyi Amfani Da Kudaden Wajen Toshe Barakar Da Annobar COVID – 19 Ta Haifarwa Makarantun.

Sunyi wannan kiran ne Ta Karkashin Kungiyar Masu Makarantu Masu Zaman Kansu Na Kasarnan APSON.

A cikin wasikar Da Kungiyar Ta Aikawa Shugaba Buhari Ta Bukaceshi Da ya Basu A Kalla Shekaru Biyar Domin Biyan Kudaden Da Zarar Gwamnatin Tarayyar ta ranta musu Kudaden.

Wasikar Dai da Suka Aikawa Ministan Ilimi Kasarnan Malam Adamu Adamu Mai Taken “Request For Stimulus Package For Private Schools Owners And Teachers”.

Wadanda Suka Sakawa Wasikar Hannu sun Hadar da, Shugaban Kungiyar Na Kasa, Dr. Godly E. Opukeme, da kuma Abdur – Rahman Marafa (Sakataren Kungiyar Na Kasa), Sai kuma Bishop Emmanuel Elakhe Wanda Shine Daraktan Gudanarwa Na Kungiyar.

Kungiyar tace Mika Bukatar tata Ta Zama Dole, Duba Da Irin Tarin Illolin Da Annobar COVID – 19 Ta Haifarwa Makarantun, Tare da Rufe Makarantun Kudi da kuma Makarantun Gwamnati da suke a Fadin Kasarnan.

To fatanmu Dai Allah Ka Gyara Mana Fannin Ilimin Wannan Kasa Tamu Mai Albarka ya tsaya Da Kafarsa yadaina Yin Rawa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button