Covid-19 ta yiwa sojojin Najeriya gagarumar ɓarna, ta kashe musu babban kwamanda.
Shugaban Sojojin Najeriya ya mutu sakamakon COVID19
Babban Jami’in Kwamandan Runduna ta 6, Fatakwal, Jihar Ribas, Maj-Gen. Johnson Olu Irefin ya mutu sakamakon rikice-rikicen da ke tattare da cutar Coronavirus.
Mutuwar kwatsam ta Irefin, wanda ya karɓi jagorancin rundunar a watan Yulin 2020 ya maye gurbin Maj.-Gen. Felix Agugo, an ce ya jefa sojojin cikin jimami.
Duk da cewa jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Manjo Charles Ekeocha, bai ce uffan ba game da rahin ba, wani babban jami’in soji daga Abuja ya tabbatar da hakan yana mai bayyana mutuwar tasa a matsayin giɓi.
Ya ce: “Daya daga cikin nagartattun jami’anmu ya mutu. Shi ne GOC na 6. Ya mutu a Abuja bayan ya yi fama da jinya sakamakon cutar coronavirus.”
Irefin ya fara aiki a matsayin kwamandan runduna ta shida da kwamandan rundunar Operation Delta Safe, Barikin Fatakwal, Irefin ya kasance tsohon GOC 81 Division Nigerian Army Lagos.