Uncategorized

Covid-19: `Yan Nigeria Su Taimakawa Gwamnati Wajen Yakar Corona Virus a Nijeria~ General. IBB

Ahmed T. Adam Bagas

Tsohon Shugaban Mulkin Sojan Nigeria Gen. Ibrahim Badamasi Babangida Ya Yi Kira `Yan Nigeria da su Taimaka kuma Su Bada Hadin kai Wajen Yakar Corona Virus a Kasar Nan, Sannan Yayi Kira ga Kiristoco Suyi Addu’a Lokacin Bikin Esta Donmin Allah ya Yaye mana wannan Cutar da Ta Addabi Kasa dama Duniya baki daya.

Sannan Tsohon Shugaban Yayi Kira ga Yan Uwa Musulmi da Suyi Tawassuli Da Kyawawan Aiyukansu Musamman Ma A Wata mai Kamawa Na Ramadan Da Nufin Allah Ya Yaye mana Wannan Cutar Ta Covid-19, Tsohon Sojan Yayi wannan Jawabin ne Lokacinda Manema Labarai Suka Ziyar Ceshi a Gidansa Dake Minna.

IBB Ya Yabawa Gwamnatocin Jahohi da mah Na Tarayya da Irin Matakan da Suka Dauka a Kokarinsu Na Dakile Yaduwar Cutar a Kasar Nan Dama Duniya Baki Daya.

Kawo Yanzu Dai A Nigeria Ansamu Mutane 318 da suke Dauke da Cutar Mutane 10 Kuma Sun Amsa Kiran Ubangiji sakamakon Cutar a Nigeria.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button