Covid-19:- Za’a Yi Sallar Jama’a Yau a Jahar Neja.
Daga Ahmed T. Adam Bagas
Gwamnan Jahar Neja Alhaji. Abubakar Sani Bello ya Bada Sanar war a Gudanar da Sallar Juma’a yau a Fadin Jahar, A Baya Bayannan Ne Dai Aka sanya Dokar Hana Zirga Zirga ko Taron Biki da Taron Ibadu Na Musulmai da Kiristoci a Fadin Jahar don Gudun Yaduwar Cutar Corona Virus a Fadin Jahar.
A Daren Jiya Alhamis ne Gwamnan ya bada Sanarwar Al’ummar Musulmi su fito suyi Sallar Juma’a Kana su koma gida Suci gaba da Killace Kansu.
Al’ummar Musulmi Na fadin Jahar Sun Nuna Farin cikinsu matuka yadda Gwamnan ya saurari Kokensu Ya Amince ya basu damar suyi sallar Juma’a a Masallatan Jahar, tun farko dai Gwamnati ta Dauki wannan matakin ne Don Gudun Yaduwar wannan Cutar ta Corona a Fadin Jahar.
Kawo yanzu dai Mutane 2 ne Hukumar NCDC ta Tabbatar suna Dauke da kwayar chutar a Jahar.