Labarai
COVID-19 zamu sake kulle Nageriya tare da Hana Shiga da fita kasashen duniya ~Lai Mohammad
Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja a wani taron tattaunawa na musamman na kamfanin dillacin labarai na Najeriya (NAN).
Mohammed, memba ne na Kwamitin Tsaro na Shugaban kasa (PTF) a kan COVID-19, ya ce yayin da gwamnati ke kula da mummunan tasirin da matsin tattalin arzikin tare da barazanar Shiga wani dokar Hana fita Yace Gwamnati zata kawar da takaita zirga-zirga zuwa da dawowa daga wasu sassan duniya ba.