Lafiya
Da Ɗumi Ɗumi: Burutai ya killace kansa saboda Covid 19.
Shugaban sojojin Najeriya janar Tukur Yusuf Burutai ya killace kansa.
Hakan ta faru ne sakamakon ganawa da sukai da wani janar ɗin Soja da korona ta kashe.
Janar Tukur Yusuf Burutai ya killace kansa tare da wasu manyan hafsoshin sojojin Najeriya a yau juma’a.
Janar Johnson olu Irefin shine janar ɗin Soja da suka shiga zaman meeting da su janar Tukur Yusuf Burutai akan matsalar tsaron Najeriya, wanda yanzu kuma korona korona ta kasheshi ƴan kwanaki kadan da taron na su.
Daga Kabiru Ado Muhd