Rahotanni

Da a Legas ne ake yawan sace sacen ‘yan makarantar nan na Arewa da tuni sun hana Gwamnati barci, in ji tsohuwar Jarumar Kannywood Mansura Isah.

Spread the love

Mansura Isah ta ce ‘yan Legas ne kadai za su iya yakar Gwamnatin Najeriya da kawo canji saboda su kadai gwamnati ke jin tsoro.

Mansura Isah ta kara da cewa ‘yan Legas na fitowa su bayyana damuwar su ba tare da wata fargaba ba, kuma kana taba daya daga cikin su kamar ka taba dukkan su ne, basa yacewa juna.

Tace babu kyashi ko bakin ciki a junan su, amma mu nan Arewa kana yin magana da wani abu ya sameka Dan’uwanka Dan Arewa kuma musulmi ne zai fara cewa Allah yakara, amma su kuwa da Abu ya samu dayansu sunta yayata abun ta ko ina har ta shafukan sada zumunta har sai gwamnatin Amurka ta shiga maganar.

Daga Kabiru Ado Muhd

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button