Da Alama Motocin Tallafin Kayan Abinci Na Shugaban Kasa Sun Fara Shiga Kano…
Daga Sabiu Danmudi Alkanawi..
A safiyar yau ne aka wayi gari da ganin wasu manyan motoci makare da kaya sunyi layi a kan titin Maiduguri Road dake Kano.
Motocin wadanda akayi hassashen sun kai guda 40 sunyi fakin ne a kusa da Iman Restaurant dake titin Maiduguri Road, har wajen kwanar Makabartar Tarauni. Sai dai kuma motocin a lullube suke yadda ba mai iya ganin abin da suke dauke dashi.
Makwabtan wajen sun shaida mana cewa basu san lokacin da aka ajiye motocin ba, su dai kawai sun gansu ne da safiyar yau.
Sai dai kuma jama’a da dama suna kyautata zaton motocin kayan abinci ne wanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi umarni da a kawo jihar Kano. Dalilin da suka kafa hujja dashi kuwa shine yanayin yadda garin na Kano yake ciki na dokar hana zirga-zirga da shige da fice.
Sai dai kuma babu wata alama da take nuna motocin na Gwamnatin Tarayya ne, don ko jami’an tsaro ma babu a wajen motocin.
Mun yi kokarin tuntubar mahukunta amma hakarmu ta gaza cimma ruwa.