Da Buhari ya sake naɗani minista a karo da tuni na kamu da Covi-19 na Mutu, in ji Solomon Dalung.
Dalilin da yasa ban yi mamaki da Buhari bai sake bani mukami ba – Solomon Dalung.
Tsohon Ministan Wasanni da Raya Matasa, Solomon Dalung, ya bayyana cewa bai yi mamaki ba da Shugaba Muhammadu Buhari bai sake nada shi ba.
Idan baku manta ba Dalung ya yi aiki a matsayin Ministan wasanni na kasa a mulki na farko na Shugaba Buhari amma an nada Sunday Dare a 2019 don maye gurbin sa.
Da yake magana a wata hira da jaridar The Punch, Dalung ya bayyana cewa ya gudanar da aikin sa ne a wa’adin mulkin Buhari na farko ba tare da neman a kara nada shi ba.
A cewar tsohon ministan, zai iya kamuwa da COVID-19 a farkon cutar idan aka sake nada shi.
Dalung ya ce: “A wurina, ina da wannan halayyar da mutane ba sa lura da ita. Ni ba mutum bane na biyu. A duk wata dama da na samu a rayuwata, ba na fatan dawowa, maimakon haka, na dauki lokaci na na yi duk abin da zan iya yi.
“Wani lokaci na kan gaya wa abokaina cewa Shugaban Tarayyar Najeriya ne ya kawo ni a matsayin minista don kada in sake dawowa a karo na biyu. Na dai tabbatar na kwashe shekaru hudun ne ta yadda in dai ba a dawo da ni ba, zan cimma abin da nake son cimmawa.
“Don haka, ban yi mamaki ba saboda nadin nufin Allah ne; idan bai nufe ku ba, baza ku samu ba. A wurina, ba abin mamaki ba ne ko kaɗan. Abin dai kawai zai taimaka wa lamiri na in fara yin tunani in ba haka ba saboda watakila idan an sake nada ni, da ban kasance da rai a yau ba.
“Idan aka yi la’akari da ofishin Ministan Wasanni da jadawalin tafiye-tafiye, watakila da na fita daga kasar a farkon wannan annoba ta coronavirus kuma babu wanda ya san abin da zai iya faruwa.
“Idan na tuna wadannan abubuwan, sai na dauki Baibul na kuma gode wa Allah da Ya kiyaye min rai.”