Da Dumi Dumi: A Halin Yanzu Tinubu Yana Ganawar Sirri Da Wike, Ibori, Makinde A Fadar Shugaban Kasa
A halin yanzu dai shugaba Bola Tinubu yana ganawa da tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Tsohon Gwamna Wike, Ibori Makinde ya isa gidan gwamnatin da misalin karfe 4:20 na yamma.
Ibori da Shugaba Tinubu sun yi gwamna tsakanin 1999 zuwa 2007, yayin da Wike ya bar mulki bayan ya cika shekaru takwas.
Wike da Makinde ‘ya’yan jam’iyyar PDP ne, kuma suna cikin kungiyar gwamnonin, G-5, da sukaki yi wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarsu, Atiku Abubakar aiki a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.
An ce Ibori ya yi wa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) aiki ne a zaben da ya gabata yayin da dan takararsa na gwamnan PDP ya sha kaye a hannun dan takarar tsohon gwamna Ifeanyi Okowa.
Akwai rade-radin da ba a tabbatar da shi ba na cewa nan ba da dadewa ba Ibori zai koma APC, bayan da ya sha kaye a hannun PDP a jihar Delta.
Wike a kashin kansa yana takun saka da shugabancin jam’iyyar PDP.