Rahotanni

Da Dumi Dumi: A Jamhuriyar Nijar An Tsawaita Dokar Hana Fita.

Spread the love

Daga Haidar H Hasheem Kano

Hukumomi a Yamai babban birnin jamhuriyar Nijar, sun sanar da tsawaita dokar hana zirga zirga dare da aka kafa a matakin dakile yaduwar cutar coronavirus.

Dokar wacce aka tsawaita da makwanni biyu zata soma aiki ne daga ranar Asabar, kuma ta tanadi hana zirga zirga daga bakin karfe 09:00 na dare zuwa 05:00 na safe a duk fadin jihar ta Yamai wacce ta fi fama da cutar corona a kasar.

A Jamhuriyar Nijar kawo yanzu dai mutane 795 ne suka harbu da cutar ta coronavirus, bayan gano wasu 14 da suka kamu.

A alkalumman da hukumomin kiwon lafiya na kasar suka fitar a jiya Juma’a, an kuma sanar da samun karin mutum biyu da cutar ta yi ajalinsu wadan ya sanya jimmilar wadanda cutar ta kashe ya yaura zuwa 44.

Baya ga hakan dai akwai mutane 600 da aka sanar sun warke daga cutar.

Hukumomin kasar dai na ci gaba da gargadin jama’a akan su kiyaye matakan da aka gindaya na dakile yaduwar cutar, ciki har da sanya takunkumin rufe fuska da kuma kaucewa tarurukan jama’a.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button