Labarai
Da Dumi Dumi- A Lagos Ankara Samun Mutuwar Mutum 3, Yayinda Mutum 22 Suka Warke.
Daga Haidar H Hasheem Kano
Gwamnatin Jahar Lages ta sanar da mutuwar mutum uku masu dauke da kwayar cutar Corona Virus a yau lahadi.
Cikin jawabin da fadar gwamnatin ta wallafa a shafukanta ta tabbatar da mutuwarsu inda ta kara da cewa an sallami mutane 22 cikin marasa lafiyar.
Yayin da cutar ta Covid-19 take kara fantsama a fadin kasar kamar wutar daji, inda jahar ta Legas tazama jahar datafi kowace jaha yawan masu dauke da cutar a fadin Najeriya baki daya.
A karshe gwamnatin tayi kira ga mutanen jahar dasu kara hakuri da wannan matsin da ake ciki kuma ta Kara bada shawarwarin cigaba da bin umarnin likitoci.