Al'adu

Da Dumi Dumi: Ahmad Nuhu Bamali Ya Zama Sabon Sarkin Zazzau.

Spread the love

Tun bayan rasuwar sarki na 18 na masarautar, Alhaji Shehu Idris, ake ta samun tashin hankali kan wanda ya zama sabon sarki.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta nada Ambasada Ahmed Nuhu Bamali Sarauta na Mallawa a matsayin sabon Sarkin Masarautar ta Zazzau.

Tun bayan rasuwar sarki na 18 na masarautar, Alhaji Shehu Idris, ake ta samun tashin hankali kan wanda ya zama sabon Sarkin.

Masarautar Zazzau tana da kananan hukumomi 11 da suka hada da Zariya, Sabon Gari, Giwa, Kudan, Makarfi, Ikara, Kubau, Soba, Igabi, Kaduna ta Arewa da kuma Kudancin Kaduna.

Ja’afaru Ibrahim Sani, Kwamishinan Harkokin Kananan Hukumomi, ya tabbatar da nadin Bamali a cikin wata sanarwar da Jaridar SaharaReporters ta gani.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da nadin Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19. Ya gaji HRH Alh. (Dr.) Shehu Idris wanda ya mutu a ranar Lahadi, 20 ga Satumbar 2020, bayan ya yi shekaru 45 yana mulki.

Ga sanarwar da Gwamnan Kaduna ta wallafa. (@GovKaduna) Oktoba 7, 2020 “Bayan rasuwar Mai Martaba, Alhaji (Dr) Shehu Idris CFR, marigayi Sarkin Zazzau na 18, Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya amince da nadin Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin na 19 Sarkin Zazzau, ”in ji Sani.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button