Labarai
Da Dumi Dumi an Sako Yara 333 da aka sace a kankara Inji Gwamnatin tarayya.
Gwamnatin Najeriya ta sanar da sakin yara maza 333 da aka sace daga makarantar sakandaren kimiyya ta Gwamnati a Kankara ta jihar Katsina.
Shugabar hukumar NIDCOM, Abike Dabiri-Arewa ce ta bayyana hakan a shafinta na Twitter.
Amma, ba ta ba da cikakken bayani game da sakin na su ba.
Tace: “Yaay, an ceto samari 333 da aka kama a katsina. Alhamdulillah!
“Gwamnatin Buhari ta dawo da yaran mu maza. KayaBackOurBoys. Yaranmu sun dawo. ”
Kuna iya tuna cewa shugaban kungiyar Boko Haram, Shekau ya dauki alhakin sace yaran makarantar.