Tsaro
DA DUMI-DUMI: An yi garkuwa da jami’an hukumar INEC a mahaifar Gwamna Matawalle suna kan hanyar zuwa Collation Center na Zamfara
An yi garkuwa da jami’in zabe na zaben gwamnan jihar Zamfara a karamar hukumar Maradun.
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin a karamar hukumar da ke mahaifar Gwamna Bello Mohammed Matawalle, wanda ke neman sake tsayawa takara.
Jami’an hukumar ta INEC sun nufi hedikwatar hukumar da ke Gusau babban birnin jihar, inda aka yi garkuwa da su aka kai su wani wuri da ba a bayyana ba.
Muktari Janyau, jami’in hulda da jama’a na hukumar INEC na jihar, ya tabbatar da rahoton ya kuma ce an kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda.