Labarai
Da Dumi dumi Boko Haram sun harbo jirgin helkwatar Nageriya
Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun harbo wani jirgin sama mai saukar ungulu na kasar Nijar dauke da wasu fasinjoji da ba a san su ba a karamar hukumar Bama da ke jihar Borno.
ta tattaro cewa lamarin ya faru ne kusa da garin Banki da misalin karfe 10 na safiyar ranar Talata kuma rahotanni sun ce mutum biyar sun mutu a hatsarin. Wata majiya ta gaggawa a Banki wacce daily trust ta ziyarci wurin tare da sojoji ta ce mai yiwuwa maharan ne ke da alhakin hatsarin inda ta ce helikofta na gwamnatin Nigerein ne.
Har yanzu sojoji ba su tabbatar da faruwar lamarin ba a lokacin rubuta wannan rahoton.
Cikakkun bayanai daga baya…