Labarai

Da Dumi Dumi Buhari ya nada Bawa Mai Shekaru 40 amatsayin Shugaban EFCC.

Spread the love

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC).

Mista Femi Adesina, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Talata.

Adesina ya ce nadin ya hau kan Hanyar tabbatarwa zuwa Majalisar Dattawa.

“Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi Majalisar Dattawa ta tabbatar da Mista Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa.”

“A wata wasika zuwa ga Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan, Shugaban ya ce yana yin aiki ne a bisa sakin layi na 2 (3) na Part1, CAP E1 na dokar EFCC ta 2004.

“Bawa, mai shekaru 40, kwararren mai bincike ne a hukumar EFCC da ke da kwarewa sosai a kan bincike da gurfanar da shari’ar rashawa ta hukuma, zambar banki, safarar kudade, da sauran laifukan tattalin arziki.

“Ya samu horo na musamman a sassa daban-daban na duniya, kuma ya kasance daya daga cikin wadanda suka yi fice a hukumar EFCC Cadet Officers a 2005. Bawa ya yi digiri na biyu na B.Sc a fannin Tattalin Arziki, da kuma Masters a Harkokin Kasa da Kasa da diflomasiyya.”

Cikakkun bayanai nan gaba ..

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button