Labarai

Da Dumi Dumi: Buhari ya umarci jami’an tsaro da su harbe duk wanda aka gani da AK-47 nan take.

Spread the love

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaro su harbe duk wanda aka gani da bindiga AK-47.

Shehu, wanda ya bayyana hakan a wata hira da BBC, ya ce shugaban ya bayar da umarnin fatattakar ‘yan fashin da suka ki mika wuya.

Dangane da kokarin da ake na kawar da ‘yan bindiga daga Zamfara da sauran jihohin arewa, Shehu ya ce gwamnati na amfani da karfin tuwo.

“Shugaban kasar ya umarci jami’an tsaro da su shiga cikin daji su harbe duk wanda suka gani da manyan makamai kamar AK-47,” in ji shi a cikin hirar.

“Ya ba da umarnin cewa duk wanda aka gani da munanan makamai a harbe shi nan take.”

Mai magana da yawun shugaban kasar ya kuma ce gwamnatin tarayya ta ayyana Zamfara a matsayin yankin da ba za a tashi da saukar jiragen ba biyo bayan bayanan sirri da ke nuna cewa ana safarar makamai zuwa ga ‘yan fashin da jiragen sama na kashin kansu.

Ya ce ana kuma amfani da jiragen wajen jigilar zinariya daga jihar zuwa Dubai, wanda, a cewarsa, ya sanya dakatar da ayyukan hakar ma’adanai kuma aka sanar a ranar Talata.

“Ana amfani da wadannan jiragen domin dibar gwal da ake hakowa a wasu yankuna na Zamfara ana fitar da su kasashen waje. Wannan yana da karfi saboda a halin yanzu, ”in ji shi.

“Akwai kasuwar zinariya a Najeriya a Dubai. Gwamnati na yin asara, mutanen kasar nan suna shan kaye, shi ya sa aka ce an hana hakar zinariya ga wadanda ba gwamnati ke yi ba. “

Haramcin ayyukan hakar ma’adanai a Zamfara an fara sanar da shi ne a watan Afrilun 2017 a daidai lokacin da rahotanni ke cewa masu hakar ma’adanan na jihar ne ke kara rura wutar matsalar tsaro.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button