Da Dumi Dumi: Da Alama Gwamnan Zai Yi Biyu Babu.
Kotu Ta Hana Obaseki Tsayawa Takarar Primary Election A PDP.
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Fatakwal Jihar Ribas ta dakatar da Gwamnan Jihar Edo daga shiga cikin zaben fidda gwani na Jam’iyyar PDP wanda aka sake tsayar da shi a ranar Alhamis, 25 ga watan Yuni, 2020.
Kotun ta kuma umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC da ta bayyana Obaseki daga dan takarar fidda gwani na jam’iyyar PDP.
Wannan ya biyo bayan karar da aka gabatar a gaban kotun mai lambar Suit No: FHC / PH / CS / 69/2020 ranar Litinin, wadda daya daga cikin masu neman takarar gwamna a PDPn Omoregie Ogbeide-Ihama, ya shigar.
Wadanda ake karar sune: Prince Uche Secondus, Emmanuel Ogidi, Hon. Kingsley Chinda, Cif Debekeme Boyleyefa, Sanata James Manaja, Hon. Barr. Ajibola Muraina, Jam’iyyar Democratic Party, Godwin Nogheghase Obaseki da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC.