Addini

Da Dumi Dumi: Ganduje Ya Gana Da Buhari Akan Hukuncin Kisan Da Aka Yankewa Wanda Yayi Batanci Ga Annabi A Kano.

Spread the love

Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi wa Shugaba Muhammadu Buhari bayani game da shari’ar saurayin dan shekara 22 da wata Kotun Shari’a ta Kano ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Idan baku manta ba Kotun Shariar ta yankewa Yahaya Sharif-Aminu hukuncin kisa bayan ta sameshi da laifi kamar yadda ake tuhumarshi.

Ana zargi Sharif-Aminu, mazaunin Sharifai a cikin birnin Kano da fadar baƙar magana ga Annabi Muhammed (s.a.w) a cikin waƙar da ya watsa ta WhatsApp a watan Maris na 2020.

Da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa a yau Talata bayan ganawa da Buhari, Ganduje ya ce ya je Fadar Shugaban Kasa ne don yi wa Buhari bayani kan batun batanci a Kano ”.

Ya ce mutanen garin sun kone gidan mahaifin wanda ake zargin “amma an tsare yaron, an gurfanar da shi a kotu, kuma an yanke masa hukuncin kisa.”

Ya ce yaron zai iya kuma ya daukaka kara a kan hukuncin. Amma, Ganduje bai bayyana matsayin shugaban kasar a kan lamarin ba.

Gwamnan na Kano ya gode wa Buhari kan taimaka wa jihar da N5bn da yayi don magance annobar da kuma sauran matsalolin tsaro a jihar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button