Labarai
Da Dumi Dumi Ganduje ya janye muƙabalar Tsakanin Abdul-Jabbar da suaram malaman Kano.
Gwamnatin Jihar Kano karkashin Dr Abdullahi Ganduje ya janye muƙabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara Wacce za a yi a ranar 7 ga wannan wata na Maris.
Wannan mataki ya biyo bayan umarnin dakatar da shirin na muƙabalar da wata kotun majistri tayi yau a kano
Gwamnatin ta ce za ta bi umarnin da kotu ta bayar domin bai dace a tsallake umarnin da kotu ta bayar ba.
A halin yanzu, gwamnatin kano ta bakin Kwamishinan shar’a na jihar Barista Abdu Musa Abdullahi Lawal ya ce babu zancen muƙabala.