Lafiya

Da dumi Dumi Ganduje ya tsige salihu tanko Yakasai Kan Buhari.

Spread the love

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya tsige mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Salihu Tanko Yakasai a kan nadin nasa kan ci gaba da kalamai da maganganun da ba a kulawa da su wadanda ake ganin sun saba wa matsayin gwamnatin All Progressive Congress (APC) da yake yi wa aiki.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, wanda ya isar da umarnin gwamnan a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, ya ce tsige war zata fara aiki nan take.

Ya ce hadimin ya kasa bambance tsakanin ra’ayin mutum da matsayar hukuma kan al’amuran da suka shafi jama’a don haka ba za a iya barin shi ya ci gaba da aiki a gwamnatin da bai yi imani da ita ba.

Gwamnan ya kuma gargadi masu rike da mukaman siyasa da ma’aikatan gwamnati da su kiyaye daga yin kalaman da za su iya haifar da rikici.

Sanarwar ta sake tabbatar da jajircewar Gwamna Ganduje kan manufofi da shirye-shiryen gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

MALAM MUHAMMAD GARBA

Hon. Kwamishinan yada labarai, na jihar Kano

27/02/2021

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button