Da Dumi dumi Genar Burtai ya tura dakarun Sojojin kwantar da tarzoma jihar legas.
Domin hana ci gaba da lalata wasu ababen more rayuwa a jihar Legas ta hanyar wasu ‘yan daba, Gwamnatin Tarayya ta tura karin jami’an tsaro don kula da dukiyar jama’a a jihar. Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana hakan a safiyar ranar Alhamis yayin da yake magana a wata hira da aka yi da shi a gidan talbijin na Arise TV wanda The PUNCH ta sanya ido a kai. Sanwo-Olu ya bayyana cewa Babban hafsan hafsoshin tsaro na jihar Gen Abayomi Olonisakin; cewa babban hafsan sojan kasa, Laftana Janar Tukur Buratai, ya kira shi a waya a ranar Laraba. Ya ce shugabannin tsaron biyu sun nemi a kara tura dakaru don tabbatar da Zaman lafiyar kadarorin jama’a
Dole ne filayen jirgin saman mu da sauran gine-ginen jama’a su aminta. ” Akwai rahotanni game da kone-kone da tashin hankali a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata yayin da wasu’ yan iska masu tayar da kayar baya suka wawashe da lalata dukiyoyin jama’a. Sanwo-Olu ya sanar da sanya dokar hana fitar ne a ranar Talata da rana sakamakon rikice-rikicen da ke faruwa a jihar. ‘Yan daba sun yi amfani da damar zanga-zangar #EndSARS kan adawa da cin zarafin’ yan sanda da kashe-kashen gilla don barna da haddasa rikici a jihar.