Labarai
Da Dumi Dumi Gwamna Ganduje ya kulle Makarantun jihar Kano.
Gwamnan jihar kano ya amince da kulle dukkanin makarantun gwamnati da masu zaman kansu a jihar nan take.
Iyaye waɗanda ‘ya ‘yansu suke a makarantun allo suma su shirya kuma su koma da yaran su zuwa gida daga gobe Laraba, 16 ga Disamba, 2020.
MUHAMMAD SANUSI S. KIRU
Hon. Kwamishinan Ilimi, na jihar Kano.