Labarai

Da Dumi Dumi Gwamna Masari ya rufe Makarantun kwana na jihar katsina.

Spread the love

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya ba da umarnin rufe dukkan makarantun sakandaren kwana da ke jihar ba tare da bata lokaci ba.

Umarnin ya biyo bayan sace wasu daliban da ba a tantance adadinsu ba na makarantar sakandaren gwamnati ta Kankara da ’yan bindiga suka yi a daren Juma’a.

Gwamnan ya yi magana ne a safiyar ranar asabar Lokacin da ya Kai ziyara tare da rakiyar Mataimakinsa Alhaji Mannir Yakubu da sauran jami’an gwamnati, suka ziyarci makarantar jihar, inda ya gana da shugabannin makarantar, da wasu iyayen yara, da shugabannin gargajiya da na addini da kuma jami’an tsaro.

Gwamnan, wanda ya kasa shawo kan Matsalar ya roki mutane da su yi hakuri da nuna juriya da fahimta, yana mai ba su tabbacin cewa gwamnati za ta yi duk abin da ya kamata don ganin an sako dukkan daliban da aka sace. Ya ce tuni jami’an tsaro, wadanda suka hada da sojoji, ‘yan sanda da kuma Ma’aikatar Tsaron Jiha suka shiga aiki kuma suna nan a kan wadanda suka sace su.

Gwamna Masari ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatocin biyu a matakin tarayya da na jiha suna iya bakin kokarin su don kawo karshen ‘yan bindiga da sauran ayyukan barna a jihar.

A cewarsa, gwamnati na da karfin gwiwa a kudurin ta na nuna rashin tausayi ga duk wata mu’amala da ‘yan ta’addan.

Sanya hannu,
Abdu Labaran Malumfashi,
DG Media.
Asabar, 12 Disamba, 2020.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button