Labarai

Da dumi dumi: Gwamnan jihar Kano ya amince da kashe biliyan 58bn domin Ayyukan inganta ruwan sha da tituna a fa’din jihar.

Spread the love

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya gabatar wa majalisar dokokin jihar Kano, ƙwarya-ƙwaryar kasafin kuɗi na fiye da Naira biliyan 58.

Shugaban majalisar Jibril Isma’il Falgore ne ya bayyana hakan yayin da ya ke karanta wasiƙar da gwamnan ya aike wa majalisar yayin zamanta na yau Litinin.

Ta cikin wasiƙar, gwamna Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci majalisar ta sahale masa kashe fiye da Naira biliyan 58 da miliyan 191 da dubu 535.

Haka kuma majalissar ta buƙaci gwamnatin Kano da ta janyo ruwan sha daga madatsar ruwa ta garin Wudil zuwa Gano da Dawakiji da kuma Zogarawa da garin Gaya zuwa Jido.

Kiran ya biyo bayan ƙudurin da wakilin ƙaramar hukumar Dawakin Kudu Shu’aibu Rabi’u, ya gabatar ya na mai bayyana cewa al’ummar yankin na fama da ƙamfar ruwan amfanin yau da kullum.

Shi ma mataimakin shugaban majalisar Muhammad Bello Ɓutu-ɓutu ya gabatar da ƙudurin neman gina titi a hanyar da ta tashi daga Mahuwa zuwa Janguza cikin gari ta dangana da garin Durum na ƙaramar hukumar Kabo.

Wakilinmu na majalisar Auwal Hassan Fagge, ya ruwaito cewa, a dai zaman majalisar na yau wakilin ƙaramar hukumar Garko Murtala Muhammad Kadaɗe, ya buƙaci zauren da ya yi kira ga bangaren zartaswa da ya sahale a samar da Ofishin hukumar kashe gobara da mota da sauran kayan aikin kashe gobara a yankin ƙaramar hukumar sa ta Garko.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button