Da Dumi Dumi Gwamnan Ondo ya ce da fulani su bar Masa jiharsa Cikin gaggawa.
Gwamna Akeredolu ya bai wa makiyaya wannan wa’adi ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Litinin.
Ya bayyana cewa su ne sanadin galibin sace-sacen mutanen da ke faruwa a jihar tasa.
“A yau mun dauki manyan matakai na warware matsalolin satar mutane a hannu daya, da kuma sauran miyagun laifuka wadanda rahotanni kan tsaro da ‘yan jarida da kuma wadanda lamarin ya rutsa da su a jihar Ondo suka yi ciakken bayani a kansu,” in ji gwamnan.
A cewarsa: “Galibin wadannan matsaloli ana danganta su da wasu bara-gurbi da ke fakewa da sunan makiyaya . Wadannan masu aikata laifuka sun mayar da dazukanmu a matsayin wuraren da suke boye mutanen da aka sace, inda suke tattaunawa domin karbar kudin fansa sannan su aikata wasu laifukan.”
Gwamna Akeredolu ya ce a matsayinsa nan babban mai kula da sha’anin tsaro na jiharsa, ba zai zue ido ba ya bari ana ci gaba da aikata irin wadannan laifuka.
“Don haka daga yau Litinin 18 ga watan Janairu, 2021 na bayar da umarnin ga makiyaya su fice daga dukkan dazukan jihar nan nan da kwana bakwai. Haka kuma an haramta yin kiwo da daddare nan take saboda da daddare aka fi lalata gonaki,” in ji shi.