Da Dumi dumi Gwamnatin jihar kaduna ta saka dokar Hana Gita a wasu sassan jihar
Ta sanya dokar hana fita a wasu sassan kananan hukumomin Chikun da Kaduna ta Kudu Gwamnatin jihar Kaduna ta ayyana dokar hana fita ta sa’o’I 24 a wasu al’ummomin yankin Kudancin Kaduna da kananan hukumomin Chikun, dokar Zata fara aiki nan take. Yankunan su ne Barnawa, Kakuri, da Talabijin a karamar hukumar Kaduna ta kudu da Maraban Rido, Sabon Tasha, Narayi da Ungwan Romi na karamar hukumar Chikun. An umarci hukumomin tsaro da su kamo tare da gurfanar da duk wanda aka samu da karya dokar hana fita da kuma wadanda ke da alhakin karya doka da oda.
An kuma umarci hukumomin tsaro da su kamo tare da gurfanar da duk wanda aka samu da wawure dukiyar Jihar. KDSG ta yi tir da Allah wadai da irin wannan harzuka da ake yi a shafukan sada zumunta. Gwamnati na kira ga dukkan al’ummomin mu da su yi watsi da tunzura su bijirewa yunkurin haifar da hargitsi da rashin zaman lafiya.