Labarai

Da Dumi dumi Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin bude Makarantun jami’a a Ranar 12 ga Octoba

Spread the love

Gwamnatin Tarayya a ranar Juma’a ta sanar da cewa ya kamata dukkan Makarantun Unity a Najeriya su ci gaba da aiki daga ranar 12 ga Oktoba. Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Abuja. A cewar Ministan, makarantu a duk fadin kasar, suna da ‘yanci don kayyade ranakun da za a fara aiki tare da tabbatar da isassun matakan tsaro. Adamu ya yi gargadin cewa makarantun da suka kasa bin ka’idojin kariya na COVID-19, to lallai rufe su za’ayi idan akwai barkewar cutar daga irin wadannan cibiyoyin.

Ya ce, “Mun yi shawarwari sosai tare da duk masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi. Idonmu da kunnuwanmu a bude suke ga kafofin yada labarai na duniya. “Na yi farin cikin bayar da rahoton cewa babu wata Mai dauke da COVID-19 a dukkan makarantun Unity. Babu mace-mace guda tsakanin ɗalibai. Mun zo ga ƙarshe cewa dole ne mu sake nazarin shawararmu. Bayan tuntuba da PTF, mun yanke shawara cewa za a bude Makarantun Unity a ranar 12 ga Oktoba, 2020. ”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button