Labarai

Da Dumi Dumi: Gwamnonin Arewa Sun isa jihar Oyo, yanzu haka suna Ganawa da gwamna Makinde akan rikicin da ya faru tsakanin Yarabawa da Hausa a Ibadan.

Gwamnonin Arewa Sun isa jihar Oyo, yanzu haka suna Ganawa da gwamna Makinde akan rikicin da ya faru tsakanin Yarabawa da Hausa a Ibadan.

Wasu gwamnoni daga yankin Arewa sun isa jihar Oyo kuma a yanzu haka suna wata ganawa ta sirri da gwamna Seyi Makinde.

Taron wani bangare ne na kokarin da ake yi don tabbatar da cewa an samu zaman lafiya bayan rikicin da ya barke a kasuwar Shasha da ke Ibadan, babban birnin jihar.

Wadanda suka halarci taron wanda ke gudana a gidan gwamnati a Agodi sun hada da gwamna Bello Matawalle (Zamfara), Abubakar Bagudu (Kebbi), Abdullahi Ganduje (Kano), da Abubakar Bello (Niger).

Ana sa ran cikakken bayani game da shawarwari a taron ba da jimawa ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button