Labarai

Da Dumi Dumi: Hukumar EFCC ta kama mutane 12 a karamar hukumar Doguwa ta Kano da Kankia ta Katsina bisa zargin sayan kuri’u a lokacin zabe

Spread the love

Mista Dogondaji ya ce an kama wadanda ake zargin ne a lokacin da suke kokarin jawo wadanda suka cancanta da kudi a wasu rumfunan zabe.

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta ce ta kama mutane 12 da ake zargi da sayan kuri’u a zaben da aka kammala ranar Asabar a jihohin Kano da Katsina.

Kwamandan EFCC na shiyyar Kano, Faruk Dogondaji, ya shaida wa manema labarai a wata hira da ya yi da su cewa, an kama wadanda ake zargin ne da tsabar kudi Naira miliyan 1.5 a jihohin Kano da Katsina.

A cewarsa, an kama mutum 10 ne a karamar hukumar Doguwa ta jihar Kano, biyu kuma a karamar hukumar Kankiya ta jihar Katsina.

Mista Dogondaji ya ce an kama wadanda ake zargin ne a lokacin da suke kokarin jawo wadanda suka cancanta da kudi a wasu rumfunan zabe.

Ya ce an kama wadanda ake zargin su 10 ne da Naira miliyan 1,357,500 a karamar hukumar Doguwa, yayin da aka kama mutanen biyu da N242,000 a karamar hukumar Kankia.

Ya ce kasancewar jami’an da ke gudanar da zaben zai kara sahihanci ga aikin.

Kwamandan na EFCC ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu bayan bincike.

(NAN)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button