Labarai
DA DUMI-DUMI: INEC ta ba da umarnin sake gudanar da zabe a yankuna tara na jihar Kogi
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayar da umarnin sake gudanar da sabon zabe a wasu unguwanni tara a karamar hukumar Ogori Magongo na jihar Kogi.
A cewar sanarwar a ranar Lahadi da ta gabata Mohammed Haruna, kwamishinan INEC na kasa kuma mamba a kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, za a gudanar da zaben a yankunan da abin ya shafa a ranar 18 ga watan Nuwamba.