Labarai
Da Dumi Dumi- Jahar Legas Ta Sallami Mutane 49 Masu Dauke Da Cutar Corona Virus.
Daga Haidar H Hasheem Kano
Gwamnatin jahar legas ta baiyana cewa a yau ta sallami marasa lafiya mutum 49 wadanda suke dauke da cutar Sarkewar Numfashi wato Covid-19.
Marasa lafiyan da dukkansu suna killace ne a gurin kula da wadanda suka kamu da cutar a fadin jahar.
Inda yanzu adadin wadanda suka warke daga cutar yazama mutum 187 fadin jahar.