Labarai
DA DUMI-DUMI: Kotu a Burtaniya ta samu Ekweremadu da matarsa da ‘yarsa da laifin safarar sassan jikin Dan’adam
Wata kotu a Birtaniya ta samu Ike Ekweremadu, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa da laifin safarar sassan jiki.
Haka kuma an samu matar sa Beatrice, diyarsa Sonia da kuma Obinna Obeta, likitan da ke da hannu a lamarin da laifi.
Alkalan kotun sun gano cewa sun hada baki ne suka kawo wani yaro Landan domin yi masa amfani da koda.
A cewar Guardian na Burtaniya, shine hukunci na farko irinsa a karkashin dokar bautar zamani.