Labarai

Da Dumi Dumi: Kotu ta umarci Gwamnatin Tarayya da ta dai-daita farashin kayan masarufi cikin kwanaki bakwai kacal

Spread the love

Babbar Kotun tarayya da ke Lagos, ta umarci gwamnatin tarayya da ta dai-daita farashin kayayyaki tare da albarkatun man fetur a ƙasar nan a cikin kwanaki bakwai.

Alkalin Kotun mai shari’a Lewis-Allagoa ne ya umarci Gwamnatin da ta saita farashin madara, fulawa, gishiri, sukari, ababen hawa, ɗai-ɗaikun kayayyakin gyare-gyare (spare parts), da makamantansu, har ma da albarkatun man fetur, irinsu desel, kalanzir, da makamansu.

Alƙalin, ya zartar da wannan hukunci ne a ranar Talata, kan shari’a mai lamba FHC/L/CS/869/2023 da fitaccen Lauyan nan, Femi Falana ya shigar a gabanta, inda ya ke ƙarar hukumar kula da farashin kayayyaki, da Atoni Janar na tarayya.

Falanan dai, ya buƙaci Kotun da ta umarci hukumar ta ƙayyade farashi da ta sauke haƙƙin da sashe na 4 na dokar ƙayyade farashin kayayyaki ya ɗora mata, na sauƙaƙa yadda farashin kayayyaki zai kasance.

Bayan sauraron hujjojin da Falanan ya gabatar kuma, Alƙalin Kotun Lewis-Allagoa, sai ya amince da dukkannin buƙatun da Falanan ya gabatar, duba da yadda waɗanda ya ke ƙarar su ka gaza bayyana a gaban Kotun, domin kare kansu.

Miftahu Ahmad Panda

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button