Labarai

Da Dumi Dumi: Kotu ta umurci DSS da su ba Emefiele damar ganin Lauyoyi da Iyalansa

Spread the love

Hukumar DSS ta kama Emefiele ne a ranar Asabar, sa’o’i bayan dakatarwar da shugaba Bola Tinubu ya yi masa a yammacin ranar Juma’a.

An umurci babban daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da DSS da su gaggauta baiwa gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) da aka dakatar, Godwin Emefiele damar ganawa da lauyoyinsa da iyalansa ba tare da bata lokaci ba kamar yadda yake a cikin hakkin sa na tsarin mulki.

Hukumar DSS ta kama Emefiele a ranar Asabar, sa’o’i bayan dakatarwar da Shugaba Bola Tinubu ya yi a yammacin ranar Juma’a.

Umarnin ya fito ne daga mai shari’a Hamza Muazu na babbar kotun birnin tarayya da ke zamanta a Maitama Abuja a ranar Juma’a, biyo bayan bukatar da J.B. Daudu SAN, Lauyan Emefiele ya gabatar.

Ya shaida wa kotun cewa ya rubuta wa DSS wasiku musamman a ranar 14 ga watan Yuni, domin neman karin umarni daga wurinsa, amma DSS ta ki amsa bukatar.

A daya bangaren kuma lauyan wadanda ake kara na biyu da na uku, I. Awo, ya shaida wa kotun cewa hukumar DSS ba ta da hurumin kin amincewa da wannan bukata, kuma yin hakan ba daidai ba ne.

Sai dai ya bayyana tabbacin hukumar tsaron za ta bi umarnin kotu tare da baiwa lauyoyin da aka lissafa da kuma iyalan Emefiele damar ganin sa, yayin da lauyan ofishin babban mai shigar da kara na kasa bai yi adawa da bukatar ba.

A wani labarin kuma, Lauyan hukumar DSS, da kuma ofishin AGF, sun bukaci a tsawaita wa’adin su gabatar da martani daban-daban kan batun da aka gabatar, wanda aka amince da shi, aka kuma dage karar zuwa ranar Talata 19 ga watan Yuni domin cigaban sauraren karar. .

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button