Labarai

Da Dumi Dumi: Kotun Sauraren Karar Zaben Shugaban Kasa Za Ta Yanke Hukunci Ranar Laraba 6 Ga Watan Satumba, Kuma Za A Watsa Zaman Kotun Kai Tsaye

Spread the love

A ranar Laraba 6 ga watan Satumba ne ake sa ran yanke hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa (PEPT) da aka dade ana jira.

Magatakardar kotun daukaka kara Umar Bangari ya tabbatar da hakan ga gidan talabijin na Channels a yau Litinin, inda ya ce za a bada damar watsa shari’ar ne kai tsaye ga gidajen talabijin masu sha’awar yin haka.

Jam’iyyun Labour Party (LP), PDP, da Allied Peoples Movement (APM) da kuma ‘yan takarar shugaban kasa, sun shigar da kara a gaban kotun da ke neman ta soke zaben shugaban kasa Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben 2023 na shugaban kasa.

Ana kuma sa ran za a yanke hukunci daga kotunan zabe a jihohi 25 na karar zaben gwamna, da na majalisar dokokin tarayya da na ‘yan majalisun jihohi.

Sakamakon zaben da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar, ana fafatawa ne a kasa da jihohi 25 daga cikin jihohi 28 da aka gudanar da zabe.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button