DA DUMI-DUMI: Kungiyar Boko Haram sun sako mata mutun 48 da suka sace a Borno
A jiya ranar laraba ne Kungiyar ta’addanci ta boko Haram sun saki Akalla matan mutun 48 da Kungiyar suka sace a kauyukan Maiwa da Shuwarin da ke karamar hukumar Mafa a jihar Borno.
Wani kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis.
Makama, yayin da yake tabbatar da ’yancin mutanen ne a dandalinsa na X wato Twitter ya ce an sace matan ne a gonakinsu a ranar Talata, 22 ga Agusta, 2023.
A cewar Makama, an kai wadanda aka sace zuwa wani wuri da ba a san inda aka kai su ba, yayin da Boko Haram suka bukaci ‘yan uwansu su biya su kudin fansa.
“A ranar Larabar jiya ne, 23 ga watan Agusta, aka sako matan bayan sun biya Naira 50,000 kowannensu a matsayin kudin fansa ga ‘yan ta’adda,” in ji manazarcin tsaron.
Makama ya kuma ce tun da farko an saki takwas daga cikin matan da aka sace bayan sun biya Naira 20,000 kowacce a matsayin kudin fansa.