Labarai

Da Dumi Dumi Nadin Sarkin Zazzau Gwamnatin Jihar kaduna tayi fatali da sunayen da aka gabatar mata Sai an sake Zabe

Spread the love

Sakataren Gwamnatin Jihar Balarabe Abbas Lawal ya bayyana cewa masu Zaben Sarakunan masarautar Zazzau a yanzu haka sun shiga wani sabon Taron gaggawa domin gano wadanda za su nemi kujerar Sarkin Fulanin 19 na Zazzau.
Hukumar ta SSG ta yi bayanin cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ta ba da umarnin sake sabon zaben ne sakamakon soke Jerin sunayen na baya da aka yi na farko, wanda akayi Babu sunan wasu
masu sha’awar sarautar wa’yanda ba’ayi Zaben dasu ba sun hada
Bunun Zazzau ya yi korafin cewa ya kasa gabatar da takardar tasa saboda an fada masa cewa an Riga an rufe karba.

Haka shima Sarkin Dajin Zazzau ya nuna rashin amincewarsa da fitar sa daga Jerin Hakanan an lura cewa masu zaben sun tantance ‘yan takara biyu a ranar 24 ga Satumbar 2020 ba tare da ganin CV din su ba wadanda masu zaben suka karba kwana daya daga baya. Hukamar ta SSG ta ce gwamnatin jihar tana ganin rashin bin ka’idar fitar da rahoton taron ranar 24 ga Satumbar 2020 kafin gwamnan ya karba.
Masu nadin sarautar dai yanzu haka suna taro don tantance dukkan yan takarar 13 da suka nuna sha’awa daga dukkan gidajen gami da guda biyu wadanda a baya aka cire su.
Rahoton wadannan tantancewar za a hanzarta mika shi ga gwamnan don ya duba, bayanin na SSG ya kammala.

Sanarwar Muyiwa Adekeye Mashawarci na Musamman ga Gwamna (Media & Communication) 30th Satumba 2020

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button