Uncategorized
Da Dumi Dumi: Ortom ya gurfana a ofishin EFCC bisa zargin karkatar da kudade
Samuel Ortom, tsohon gwamnan jihar Benuwe, ana yi masa tambayoyi a ofishin hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC.
Tsohon gwamnan yana ofishin shiyya na hukumar EFCC da ke Makurdi, babban birnin jihar.
Majiyoyin da ke sa ido kan ci gaban sun shaida mana cewa Ortom ya isa cibiyar hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa da safiyar Talata.
Ana tuhumar Ortom ne bisa zargin almubazzaranci da dukiyar al’umma a lokacin da yake gwamnan jihar.