Labarai
Da Dumi dumi Shugaba Buhari na Ganawar sirri da Jami’an tsaron Nageriya
Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), da shugabannin tsaro na kasar a halin yanzu suna ganawa a fadar Villa, Abuja. Ministocin masu ruwa da tsaki kuma suna halartar taron Majalisar Tsaron Kasar.
Manyan hafsoshin tsaron da suka halarci taron sun hada da shugaban hafsin tsaro, Janar Gabriel Olonisakin; Shugaban hafsin soji, Laftanar Janar Tukur Buratai; Shugaban hafsan sojojin ruwa, Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas; Shugaban hafsan sojin sama, Air Marshall Sadique Abubakar; Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu; Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa, Ahmed Rafa’i Abubakar; da Darakta-Janar na Daraktan Ayyuka na Jiha, Yusuf Bichi.
Cikakkun bayanai suna Zuwa…