Da Dumi Dumi : ‘Tallafin Man Fetur Ya Kare – Shugaban Kasa Tinubu

Spread the love

Sabon shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce zamanin biyan tallafin man fetur ya kare.

Ya ce kasafin kudin shekarar 2023 bai yi tanadin tallafin man fetur ba, haka ma, biyan tallafin ba shi da tushe balle makama.

“Tallafin mai ya tafi,” in ji Tinubu a jawabinsa na farko a dandalin Eagle Square a ranar Litinin bayan an rantsar da shi a matsayin shugaban Najeriya na 16.

Tinubu ya ce a maimakon haka gwamnatinsa za ta rika ba da kudade zuwa ababen more rayuwa da sauran fannoni don karfafa tattalin arzikin kasarnan, inda ya kara da cewa “daidaitaccen kudin musaya” ya ba shi tabbacin a karkashin gwamnatinsa.

Ya kuma yi alkawarin sake fasalin tattalin arzikin kasarnan domin kawo ci gaba tare da habaka tattalin arzikin cikin gida ta hanyar samar da ayyukan yi.

Tinubu ya kuma sha alwashin kawar da Najeriya daga ta’addanci da aikata laifuka.

“Tsaro ne zai kasance kan gaba a gwamnatinmu,” in ji shi, inda ya kara da cewa zai sake fasalin gine-ginen tsaro, zai kara saka hannun jari kan jami’an tsaro, ingantacciyar horarwa da samar da ingantattun kayan aiki ga jami’an tsaro.

Sabon Shugaban ya ce zai kawo karshen talauci da fatara, zai wadata abinci, tabbatar da shigar mata da matasa gwamnatinsa tare da hana cin hanci da rashawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *