Labarai

DA DUMI-DUMI: Tinubu ya gana da ’yan kasuwar mai kan cire tallafi

Spread the love

Taron dai na zuwa ne kimanin kwanaki 10 bayan da shugaban kasar a jawabinsa na farko ya bayyana cire tallafin man fetur.

A ranar Laraba ne shugaban kasa Bola Tinubu ya gana da manyan ‘yan kasuwar mai a Aso Rock da ke babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.

‘Yan kasuwar sun samu jagorancin Gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun, wanda shi ne Shugaban kungiyar masu sayar da mai.

Ganawar da shugaban kasar ya yi da ‘yan kasuwar mai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce da zanga-zangar da ta biyo bayan cire tallafin Man Fetur.

Shugaban kasar a yayin jawabinsa na farko a ranar 29 ga watan Mayu a dandalin Eagle Square da ke Abuja ya sanar da cire tallafin man fetur. Shugaban ya ce gwamnatin da ta shude ta Muhammadu Buhari ba ta yi tanadin tallafi a kasafin kudin 2023 da ya wuce watan Yuni ba.

‘Yan Najeriya da dama sun yi tsammanin cewa sabon tsarin farashin zai fara aiki a ranar 1 ga watan Yuli amma kusan nan da nan bayan sanarwar shugaban kasar, sai ga layukan da suka sake kunno kai a gidajen man da ke fadin kasar duk da cewa gidajen sayar da kayayyaki na tara kayan da kuma kara farashin.

Tuni dai ana siyar da litar man fetur sama da N500 a fadin kasar nan biyo bayan daidaita farashin kamfanin na NNPC da kuma sanarwar cire tallafin da shugaban kasa ya yi.

Tun daga lokacin da layukan man fetur suka yi ta karuwa ga muhimman kayayyaki, lamarin da ya kara tabarbarewar zirga-zirgar ababen hawa a sassan kasar, duk da cewa farashin sufuri ya yi tashin gwauron zabi sama da kashi 100.

Kungiyar Kwadago ta yanke shawarar fara yajin aikin ne a fadin kasar daga ranar Laraba, sai dai wata kotu ta hana ta a ranar Litinin 5 ga watan Yuni, 2023. Daga bisani kungiyar kwadagon ta janye yajin aikin da ta shirya yi bayan wata ganawa da gwamnatin tarayya da yammacin Litinin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button