Labarai
Da Dumi Dumi: Wani matashi ya kashe mahaifiyarsa ta hanyar caka mata wuka a Kano
Wani matashi mai suna Iro Kwarangwal ya daba wa mahaifiyarsa, Jummai wuka inda ya kashe ta har lahira saboda rashin jituwar dake tskaninsu a jihar Kano.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Laraba a Karshen Kwalta da ke unguwar Rimin Kebe a karamar hukumar Ungogo ta jihar.
“Ina tsaye a wajen gidana, kwatsam na ji kururuwa daga gidan marigayiyar,” wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa manema labarai.
Ya bayyana cewa da ya garzaya domin bada agaji, ya tarar da marigayiyar tana kururuwar neman agaji a cikin jininta.
Shaidan gani da ido ya bayyana cewa wanda ake zargin ya gudu daga wurin jim kadan bayan da ake zarginsa da aikata munanan laifuka ga mahaifiyarsa kamar yadda Daily Nigerian ta rawaito.