Labarai

Da dumi dumi ‘yan Bindiga sun dawo sun kashe mutun Hudu 4 sun Kuma Sace mutun 11 a kagara.

Spread the love

Akalla mutane hudu aka kashe a wasu sabbin hare-hare a Kagara da ke jihar Neja Al’umma sun kasance cikin dar-dar tun ranar 17 ga Fabrairu, 2021, lokacin da wasu gungun masu dauke da makamai suka sace ma’aikata da daliban Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati, Kagara.

An saki wadanda lamarin ya rutsa da su a daidai lokacin da labari ya bazu kan sabbin hare-hare a Kagara.

Bayanai daga Kagara sun shaida wa majiyarmu cewa an yi garkuwa da mutane 11, ciki har da mata bakwai a wasu kauyuka daban-daban.

An ce ‘yan bindigar sun kai hari Gidan Adamu, kusa da Yakila, hedkwatar gundumar Gunna.

Tun da farko an sace Hakimin Yakila yayin da ba a san inda yake ba.

Majiyar ta kuma shaida wa wakilinmu cewa barayin sun far wa wani kauye da ake kira Gidan Wamban Karaku suka yi awon gaba da mata bakwai, biyu daga cikinsu uwaye masu shayarwa.

Sun kuma sace shanu masu yawa, in ji majiyar.

Haka kuma a gundumar Madaka, sun yi garkuwa da Limamin kauyen Rubo kamar yadda majiyar ta ce.

Kamar yadda a lokacin wannan rahoton, ana binne wadanda suka mutu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button