Da Dumi Dumi ‘Yan Bindiga sun kashe mutun uku 3 sun Sace mutun daya 1 a Jihar Kano.
Wasu ‘yan bindiga sun afka wa kauyen Rurum da ke karamar hukumar Rano da misalin karfe 1 na ranar Talata inda suka yi awon gaba da mahaifiyar wani dan kasuwa, Alhaji Yusuf Jibrin.
Wani mazaunin garin ya tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun bude wuta, wanda ya yi sanadiyyar kisan mutane uku da kuma sace Alhaji Yusuf Jibrin da matar sa, Hajiya Asabe Jibrin amma daga baya suka saki mijin.
Ya kuma ce an harbe dan uwan nasa amma daga baya ya mutu da yammacin Laraba a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, yayin da sauran wadanda abin ya shafa ciki har da tsohon da ya tsere daga hannunsu ke karbar kulawa.
Ya kara da cewa hukumomin tsaro ba su iso wurin ba sai bayan sun gama aikin. Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce ‘yan bindigan sun yi awon gaba da mutane biyu amma sun kubutar da daya kuma suna kan hanya don tabbatar da cewa an kuma ceto sauran.
Harin na zuwa ne kasa da mako guda bayan sabon kwamishinan ‘yan sanda ya hau mulki.
Rahotan Sehelian Times