Tsaro

Da Dumi Dumi: ‘Yan Bindiga sun sace Ɗalibai a Kaduna.

Spread the love

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu satar mutane ne sun kai hari a Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya da ke Jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da dalibai da dama.

Kwalejin tana nesa kaɗan da Kwalejin Tsaro ta Najeriya a yankin Mando na Jihar Kaduna.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige ya fada wa gidan talabijin na Channels cewa maharan sun mamaye kwalejin da ke yankin Mando a wajen garin Kaduna da misalin karfe 3 na safiyar Juma’a suka yi awon gaba da wasu daliban.

Sai dai ya ce ba a tabbatar da ainihin adadin daliban da aka sace ba.

Ya bayyana cewa an taura jami’an tsaro zuwa kwalejin da suka ji labarin harin kuma sun sami damar tsare sauran daliban.

Kakakin ya kuma ce ana ci gaba da bincike don gano ainihin adadin daliban da aka sace da nufin bin sawun ‘yan bindigar tare da kubutar da wadanda abin ya shafa.

Wannan sabon satar ta zo ne sa’o’i 48 bayan Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan, ya gabatar da rahoton halin tsaro na shekarar 2020 ga Gwamna Nasir El-Rufai.

Aruwan ya ce ‘yan ta’addan sun kashe akalla mutane 937, sun yi garkuwa da mutane 1,972 a cikin jihar a shekarar 2020.

A nasa bangaren, Gwamna El-Rufai ya yi watsi da yiwuwar gwamnatinsa ta sasanta ko kuma yin afuwa ga ‘yan ta’addan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button