Labarai
Da Dumi Dumi ‘yan bindiga sun Sace dan uwan ministan Noma
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu satar mutane ne sun kai hari gidan dangin Ministan Noma, Sabo Nanono, inda suka yi awon gaba da dan uwansa, Babawuro Tofai.
Mai taimaka wa Ministan na musamman, Umar Wali, wanda ya tabbatar da satar ga Solacebase ya ce ‘yan bindigar sun kai hari gidan da misalin karfe 1.00 na rana
Kafin sace Babawuro Tofai, wani karamin yaro a cikin gidan ma an buge shi kuma ya samu karaya yayin harin, ’’ in ji Mista Wali. A cewarsa, har yanzu maharan ba su tuntube shi ba. ~Rahotan daily Nigerian