Tsaro

Da dumi dumi ‘yan Bindiga sun sake Kai hari ga daliban Makaranta a ikara ta jihar kaduna

Spread the love

‘Yan bindiga sun kai hari makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati, Ikara a jihar Kaduna.

Majiyarmu ta tattaro cewa wasu mutane dauke da muggan makamai sun mamaye makarantar da safiyar yau Lahadi amma sojoji sun dakile shirinsu na sace daliban, kamar yadda Samuel Aruwan, Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida ya bayyana.

Aruwan ya tabbatar da cewa dukkan daliban makarantar 307 na cikin aminci da tsaro.

“Yunkurin satar ya ci tura. Abin farin cikin shine, daliban sunyi amfani da tsarin gargadi na tsaro kuma don haka sun sami damar fadakar da jami’an tsaro. Jami’an tsaron sun hada da sojojin Najeriya da ‘yan sanda tare da wasu jami’an sa kai na tsaro cikin hanzari suka nufi makarantar don tunkarar’ yan ta’addan, sojoji da ‘yan sanda suna bin sawun’ yan ta’addan, “in ji shi

Lamarin ya faru ne kwanaki biyu bayan an sace dalibai 39 daga Kwalejin Koyon Gandun Daji ta Tarayya da ke Afaka, karamar hukumar Igabi ta jihar.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar suna kan hanyar zuwa makarantar sakandare amma da suka samu labarin an tsaurara matakan tsaro a inda suka nufa, sai suka mamaye makarantar.
Cikakkun bayanai daga baya…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button