Da Dumi Dumi: Yan Majalisun Najeriya sun amince da ƙudurin dokar da zata bawa Gwamnati damar bawa ɗalibai bashi domin suyi karatun gaba da Sakandare, wato “Students’ Loan, Access to Higher Education.

“Yan Majalisun Najeriya sun amince da ƙudurin dokar nan da zai bawa Gwamnati damar bawa ɗalibai bashi don suyi karatun gaba da Sakandare, wato “Students’ Loan, Access to Higher Education Act” yanzu kawai Shugaban ƙasa za’a jira don ya sanya ma dokar hannu Shikenan”
Shin wai Kun san me ake nufi da Student Loan kuwa ?
Student Loan wani tsari ne da gwamnatin Najeriya ke son ɓullowa dashi na bawa ɗalibai bashi domin su cigaba da karatun su na gaba da Sakandare, kazalika bashin ana bayar dashi ne ga ɗalibin da yake karatu a Najeriya kama tun daga matakin Diploma har zuwa Degree.
A Shekarar 2019 Femi Gbajabiamila ya gabatar da ƙudirin dokar da yake so a riƙa bawa ɗalibai bashi domin su samu suyi karatun gaba da Sakandare, wanda hakan yake nuna cewa gwamnati zata daina ɗaukar Nauyin ilimin gaba da Sakandare kenan baki ɗaya, zai zama duk wanda zaiyi karatun to sai ya riƙa biyan kuɗin Makaranta, kuma ana hasashen kuɗin zai iya farawa daga 500k zuwa sama, ya danganta da Course din da ɗalibi zai karanta ne.
Yadda tsarin yake shine:
—Gwamnati zata ƙirƙiri Banki mai suna “Nigeria Education Bank” Wannan bankin shine aka ɗora ma alhakin baiwa ɗalibai bashin.
—Duk ɗalibin da zai karɓi wannan bashin za’a buɗe masa asusun ajiya da wannan bankin a ƙarƙashin Student Funds.
—Duk ɗalibin da yake so ya karɓi bashin zai rubuta takarda ne zuwa ga Chairman na Bankin, ta hannun Students Affairs Division.
—Ita kuma Makarantar zata tattara sunayen ku gaba ɗaya ta rubuta Cover Letter ta tura ma Chairman na Bankin a cikin kwana 30.
—Ba za’a bawa ɗalibin bashi ba har sai idan ya zama a Shekara gidan su basa samun kuɗin da yakai 500k.
—Ba za’a bawa ɗalibi bashin ba har sai ya kawo Guarantors (Masu lamuni) mutum biyu, kowannen su ya zama Ma’aikacin gwamnati ne da yake mataki na 12 zuwa sama (Level 12 to above) KO kuma lauyan da ya shekara aƙalla 10 yana aikin lauya.
—Ba za’a bawa ɗalibi bashin ba idan ya zama ya taɓa cin bashi bai biya ba.
—Ba za’a bawa ɗalibi bashin ba idan aka kama shi ko kuma an taɓa kama shi da laifin Satar Jarabawa (Examination Malpractice)
—Ba za’a bawa ɗalibi bashin ba idan an taɓa kama shi da laifin yaudara ko zamba cikin Aminci.
—Ba za’a bawa ɗalibi bashin ba idan an taɓa kama shi da laifin ta’ammali da miyagun kwayoyi.
—Dole ne Makarantar ta tabbatar ta tura takardar duk ɗalibin da yake neman bashin kwana 30 da rufe Admission ɗin su.
—Za’a tura ma kowanne ɗalibi kuɗin ne kwana 30 da tura sunayen su zuwa ga bankin.
—Duk ɗalibin da ya karɓi bashin zai fara biya ne Shekara biyu da gama Service ɗin shi (wato NYSC)
—Gwamnati zata cire kuɗin ne kai tsaye daga Asusun ka na banki, sannan zata riƙa cire 10% ne na Albashin ka.
—Idan kuma ba aikin Gwamnati kake yi ba to dole zaka riƙa tura masu 10% na ribar da kake samu duk wata, sannan za ka fara biyan su ne bayan wata biyu
—Idan kuma kaki biya ka aikata laifi, za’a ɗaure ka na tsawon Shekara biyu kuma ka biya tarar kuɗi 500k.
To Wannan shine tsarin da ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa ASUU take adawa dashi tuntuni, amma mutane sun kasa Fahimtar ta sai suna ganin tana yaƙi ne kawai don Aljihun ta, alhali kuma ba haka bane, kasancewar duk mai bibiyar al’amuran yau da kullum ya san irin illar da wannan bashin yake haifarwa, wanda kuma bai sani ba to yaje ya bincika ƙasar America da Suka bada irin wannan bashin yaya makomar ɗaliban ta kasance bayan sun gama karatun, duk da su fa suna cikin Developed Country to bare kuma mu Najeriya !
Bissalam
Shehu Rahinat NaAllah